Tsibirin Shaidan Ko Tsibiri Bermuda Tsibiri Ne Da Labarinsa Ke Da Matukar Daukar Hankali

TSIBIRIN BERMUDA KO TSIBIRIN SHAIƊAN

Tsibirin Shaiɗan da ake wa laƙabi da "Bermuda Triangle" a Turance, tsibiri ne da  labarinsa ke matuƙar ɗaukar hankalin masu saurare. An sha bayyana labarinsa a cikin tatsuniyoyi da almara. A kodayaushe, akan bayyana abubuwan ban al'ajabi da ke faruwa a cikinsa. Daga cikin abubuwan al'ajabin da aka bayyana a wannan tsibiri na shaiɗan akwai wasu irin halittu da har yanzu ba a tantance ko waɗanne irin halittu ba ne. Sannan akwai Aljanu da dabbobi iri-iri. Wasu ma har sukan bayyana tsibirin da fadar shaiɗan. Wato a tasu fahimtar, karagar mulkin shaiɗan a nan take.

 A INA TSIBIRIN BERMUDA YAKE?

Masana da dama sun sha bayyana cewa tsibirin shaiɗan da ake wa laƙabi da "Bermuda Triangle" na nan a yammacin kogin Atlanta tsakanin  Florida, Puerto-Rico da Bermuda. A nan ne aka bayyana cewa wannnan fada ta Shaiɗan take. Ana yi masa laƙabi da fadar shaiɗan ne saboda al'ajabin da ke faruwa a cikinsa. Sai dai shahararren mai kuɗin nan kuma masanin kimiyya da fasaha na ƙasar Amurka wato Elon Musk ya bayyana cewa shi fa sam bai ga wani abun al'ajabi a tattare da tsibirin Bermuda ba. A mahangarsa, ya bayyana wa duniya cewa kogin Atlanta da Bermuda Triangle ke cikinsa, kamar sauran koguna ne, kawai dai kogin yana da sarƙaƙiyar igiyar ruwa da kuma haɗarin yanayin ƙasa (Fashewar iskar gas daga ƙasan tekun) Sai kuma kura-kuren da ɗan'Adam ke aikatawa a yayin kewaya kogin wanda hakan ke jawo ɓacewar jiragen sama da kuma nutsewar jiragen ruwa.


A taƙaice dai Bermuda Triangle, wanda ake kira da "Triangle na Bermuda" ko "Yankin Bermuda," wani yanki ne a cikin Tekun Atlantika wanda aka yi imanin cewa yana da alaƙa da bacewar jiragen ruwa da jiragen sama da yawa ba tare da wani dalili ba.

ABUBUWAN DA YA KAMATA A SANI GAME DA TSIBIRIN BERMUDA
 
· Yana tsakanin Bermuda, Florida (Amurka), da Puerto Rico
· Yana da siffar (triangle)
· Yankin ya shahara saboda labarai da almara game da ɓacewar jiragen ruwa da na sama

ABUBUWAN DA SUKA FARU

· An ba da rahoton ɓacewar jiragen ruwa da na sama da yawa a cikinsa
· Ɗaya daga cikin shahararrun al'amuran shi ne ɓacewar "Flight 19" a shekarar 1945
· Wasu jiragen ruwa sun ɓace ba da wata sanadiya ba

DALILAN FARUWARSU

· Wasu masana sun bayar da hasashe na halitta kamar iskar gas, canjin yanayi, ko sauran abubuwan da ba a saba gani ba
· Wasu kuma sun ce al'amuran sun faru ne saboda halayen yanayin tekun da kuma iskar yankin

SHIN, LABARIN TSIBIRIN BERMUDA GASKIYA NE KO KARYA?

· Yawancin masana sun nuna cewa yawancin al'amuran na iya zama na halitta ko kuma an yi kuskuren bayar da rahoto
· Hukumar kula da teku ta duniya ba ta amince da Bermuda Triangle a matsayin wani yanki na haɗari na musamman ba

Kodayake Bermuda Triangle ya zama wani abu mai ban al'ajabi a cikin al'adun jama'a, yawancin masana suna ganin cewa babu wani abu na sihiri ko na allahntaka game da yankin.

1 Comments

  1. Lallai tsibirin Shaidan ko tsibirin Bermuda, tsibiri ne da ke da matukar daukar hankalin masu saurare.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post