Wata kotun soji a Kamaru ta yankewa sojoji uku da wani ɗan ƙungiyar sa-kai hukuncin ɗaurin kurkuku bisa samunsu da laifin kashe akalla fararen hula 21 a yankin Arewa maso Yamma mai rinjayen masu magana da Turanci.
Lamarin ya faru tun watan Fabrairun 2020 a ƙauyen Ngarbuh, amma shari’ar ta shafe kusan shekara shida ana yi kafin yanke hukunci.An same su da laifukan kisa da ƙone dukiya da lalata kadarori, inda aka yanke musu hukuncin zaman gidan yari tsakanin shekara biyar zuwa goma.
Wannan hari na daga cikin lokuta kaɗan da gwamnati ta amince dakarunta sun aikata laifi, domin a farko hukumomi sun musanta hannu a lamarin kafin daga bisani suka amince bayan matsin lamba daga ƙasashen duniya.
Lauyoyin waɗanda abin ya shafa sun bayyana rashin gamsuwarsu da hukuncin, suna cewa girman laifin da aka aikata ya kamata a zartar da hukunci mafi tsauri fiye da haka.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun sha zargin ɓangarorin biyu, wato ’yan aware da dakarun gwamnati, da aikata ta’asa tun bayan ɓarkewar rikicin yankunan masu magana da Turanci a 2017.
A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, rikicin ya yi sanadin mutuwar akalla mutane dubu shida tare da raba sama da rabin miliyan da muhallansu.