Antony Ya Kwato Wa Betis Maki Daya

Tsohon ɗan ƙwallon ƙungiyar Manchester United Antony D. Santos shi ne ya farke ƙwallo ta biyu da aka zura a ragar ta Real Betis tun a mintuna 23 na farkon rabin lokaci a wasan Europa League.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafar Real Betis ta karɓi baƙuncin ƙungiyar ƙwallon ƙafar Nottingham Forest a daren yau Laraba, inda ɗan wasan Forest ɗin Jesus ya zura ƙwallaye biyu a ragar Betis a mintuna na 18 da kuma 23. Bayan da Bakambu ɗan ƙwallon Betis ya zura ƙwallo ta farko a ragar Forest tun a mintuna 15 da fara wasan.
Haka aka ci gaba da wasan Forest na jan ragamar wasan har zuwa mintuna 85 inda Antony sabon ɗan wasan da suka sawo ya zura masu ƙwallo wadda ta mayar da wasan ɗanye tare da samo masu maki guda, kuma wannan ce ƙwallonsa ta farko tun bayan fara wasansa bayan kammala cinikin nasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post