An Bankado Ma'aikatan Bogi

''Gwamnatin jihar Katsina ta bankaɗo ma'aikatan bogi mutum dubu uku da ɗari huɗu da tamanin da takwas 3,488 a ƙananan hukumomi 34 da kuma na LEA's da ke a jihar Katsina. A cikin ma'aikata dubu hamsin da ɗari ɗaya da saba'in da biyu 50,172 da aka tantance, sakamakon tantancewar zai sa gwamnatin jihar Katsina ta riƙa samun rarar Kuɗi da suka kai darajar naira miliyan ɗari huɗu da hamsin da uku (453) a duk watan duniya.'' In ji shugaban kwamitin tantancewar Alhaji Abdullahi Gagare.

Post a Comment

Previous Post Next Post