Tun bayan sasancin da aka yi a ƙaramar hukumar Musawa, wasu mutanen ke ci gaba da kwanciya cikin ɗarɗar da firgici a cikin gidajensu, yayin da wasu kuma suke yin barci har da saleɓa.
Tun daga ranar da aka yi wannan sulhun, har zuwa yau da muke rubutun nan ba a samu tsagaitawar kai hare-hare a ƙaramar hukumar ta Musawa ba. Domin za mu iya tunawa, a ranar da aka yi sulhun ma, bayan an tashi daga wurin sulhun, cikin dare sai ga 'yan ta'adda sun bayyana a wani ƙauye mai suna 'Yarkanya, inda suka ɓarje gumensu kuma suka tafi da mutane domin neman kuɗin fansa.
Daga Nan Sai Me Ya Faru?
Ko da aka tuntuɓe su cewa an yi sulhu da su fa, amma me ya sa haka take faruwa? Sai suka kada baki suka ce, su ba su suka aikata wannan ɓarnar ba, amma za su bincika su dawo da mutanen da aka tafi da su. Sai dai har yanzu ɗin nan babu tabbacin dawowar mutanen bare dukiyoyinsu. Wata majiyar kuma cewa ta yi sun ce. 'Ba mu san nan ma ƙaramar hukumar Musawa ba ne.'
An Yi Wa Tufkar Hanci?
Washen garin abin da ya faru a 'Yarkanya, sai muka ji ɓullarsu a ƙauyen Ɗanjanku, can ma sun dira, suka yi ɓarnarsu son ransu, suka kwashi shanayen al'umma masu ɗumbin yawa suka kora su zuwa daji kamar kayan gado.
Nan ma ba a yi ƙasa a gwiwa ba, aka tuntuɓe su tare da tunatar da su batun sasancin da aka yi da su. Amsar dai da suka bayar duk iri ɗaya ce, 'Ba mu, ba ne, amma za mu yi ƙoƙarin gano ko su wane ne, kuma a maido da shanun da aka tafi da su.
Sun Cika Alƙawari!
A wannan al'amari na Ɗanjanku kuwa, sun cika alƙawarin da suka ɗauka, domin sun dawo da fiye da rabin shanun da suka kore, sauran kuma suka ce, sun yi nisa a daji, ba za a iya dawowa da su ba, sai dai a rungumi sorry.
Ko Abin Ya Tsaya Daga Nan?
Bayan 'yan kwanaki, sai ga su sun sake dira a garin Jikamshi, wanda shi ne babban gari a duk faɗin ƙaramar hukumar ta Musawa a daren Litinin wajen ƙarfe 11:35. Sun daɗe suna ba-ta-kashi da 'yan bijilanti da 'yan sandan da suka kawo ɗauki, amma duk da haka sai da suka ɗauki mutane biyu, mace ɗaya namiji ɗaya, dukkansu kuma magidanta ne.
Bayan kwana ɗaya sai ga wayarsu, sun ce sai an kai masu Naira Milyan ɗari biyu, sannan su sako su. Abin da zai tayar maka da hankali shi ne, ita fa matar da aka ɗauka, da ma can an taɓa ɗaukar mijinta, ko da suka ɗauke ta a Jikamshi tana matsayin 'yar gudun hijira ce, amma duk da haka ba su tsira da sharrinsu ba.
Kwana ɗaya bayan faruwar wannan sai muka samu rahoton an gan su a wani ƙauye da ake kira Jama'a da yake a ƙaramar hukumar Matazu. Bayan 'yan wasu lokuta kuma sai ga su a 'Yarkanya ta ƙaramar hukumar Musawa sun tsallaka titi sun shiga wani ƙauye da ake kira Ɗorayi, a can ne fa suka yi ɓarna iya ɓarna, domin sun kore shanayen da suka fi 150. Sai dai kwana ɗaya bayan faruwar hakan an shaida mana cewa, an ga wasu shanu da ba su wuce guda 17 ba sun dawo gida da kansu. A ranar dai suka shiga ƙauyukan Sabon Garin Garu suka kashe mutane shida a ciki har da jaririn da ake shayarwa saboda zalunci.
A daren jiya kuma Talata, sai ga su sun ɓulla ƙauyen Bachirawa da ke ƙaramar hukumar Musawa inda nan ma suka ɗauki mutane biyu mace da namiji da nufin amsar kuɗin fansa.
Duka waɗannan abubuwan da na zayyano sun faru ne cikin kwanakin da ba su wuce mako biyu ba.
Albarkacin Bakin Mutanen Yankin!
Da yawan al'ummar yankin suna Allah wadai da wannan sasanci, har ma wasu na kallonsa a matsayin shashanci ko ma wata hanya da aka buɗewa 'yan ta'adda su idasa sanin abin da ba su sani ba.
Domin sasanci ne da aka yi ba tare 'yan ta'addar nan sun ajiye ko da allura ba, bare wuƙa ko bindiga. Sannan sasancin ya ba su dama suka riƙa shiga garuruwa suna abin da suke so, wai don a yi sabo da su.
Da yawan mutane suna tsoro da fargabar kar fa wannan sasancin ya zamo silar afkawar waɗannan 'yan ta'adda maƙwabtan ƙananan hukumomin da ba a yi sasanci da su ba, domin idan an lura abin fa haka yake tahowa suna ta ƙara mamaye yankuna da ƙananan hukumomi. Saboda muddin aka yi sasancin da ku, to kuwa ko da za ka gansu a hanya sun yo sata, kai fa ba za ka ce uffan ba, bare ka ɗauki mataki, sai dai ka ba su hanya su wuce idan ma da hali har ruwan gora ka siya ka ba su tare da yi masu ban gajiya da wannan gagarumin aiki da suka yi.
Fatanmu!
Muna fata da roƙon Allah ya kawo mana sauƙi a cikin wannan al'amari, sannan muna kira ga gwamnati da ta ƙara yin iya bakin ƙoƙarin da take yi don ganin irin haka bai ci gaba da faruwa ba, ta hanyar rarraba ma'aikata zuwa yankunan da waɗannan abubuwan suka fi ta'azzara da dai duk wani mataki da take ganin zai kawo ƙarshen wannan masifa.