Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa Ph.D ya rantsar da sabbin masu ba shi shawara guda biyu a safiyar yau Laraba.
Inda aka rantsar da Honourable Tasi'u Ɗahiru
Ɗanɗagoro, tsohon kwamishinan ayyuka da gidaje da zirga-zirga na lokacin mulkin tsohon gwamnan Katsina
mai girma Alhaji Aminu Bello Masari. An rantsar da shi a matsayin mai ba wa gwamna shawara a fannin karatun Alƙur'ani mai girma da kuma yaran da ba su zuwa makaranta.
An kuma rantsar da Honourable Aminu Lawal Jibia, a matsayin mai ba wa gwamna shawara a ɓangaren ci gaban al'umma.
Honourable Aminu Lawal Jibia shi ne tsohon shugaban ƙaramar hukumar Jibia a shekarar 2013-2015. Ya kuma riƙe muƙaman mai bayar da shawara a harkokin ayyuka da harkokin bayar da horo na ƙananun kasuwanci da ɓangaren harkokin ci gaban al'umma a shekarun 2016 zuwa 2019, 2019 zuwa 2022.
Tags
Siyasa