Masarautar Daura Karkashin Jagorancin Sarkin Daura Faruk Umar Faruk Ta Nada Dauda Kahutu Rarara A Matsayin Sarkin Mawakan Kasar Hausa

DAUDA ADAMU KAHUTU RARARA

Shahararren mawakin nan dan asalin jihar Katsina kuma haifaffen kauyen Kahutu da ke karkashin garin Danja ta Jihar Katsina da ya shahara a fagen wakokin Hausa musamman na siyasa ya samu nasarar zama sarkin mawakan kasar Hausa, biyo bayan nadin da sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk ya yi masa a yau Alhamis 25/09/2025.


Idan ba a manta ba kwanaki kaɗan da suka wuce an hango bidiyo da hotunan mawaƙin a wata jami'a mai suna European-American University da ke Panama a yayin da yake amsar takardar shaidar girmamawa ta digirin digirgir wadda ta jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta. Yau kuma sai ga shi kwatsam an hango shi a Daura, fadar mai martaba Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk wajen amsar naɗin sarauta da aka yi masa.

MASARAUTAR DAURA 

Masarautar Daura ce ake kira "Uwar Masarautun ƙasar Hausa Bakwai". Saboda tarihi ya nuna cewa ita ce farkon cibiyar da aka kafa daga cikin masarautu bakwai na asali. Kuma daga gare ta ne aka samu kafuwar garuruwan Hausawa kamar su:

1. Daura:
2. Kano
3. Rano
4. Zazzau (Zaria)
5. Gobir
6. Katsina
7. Biram (Hadejia)

Saboda haka, dukkan sarakunan waɗannan masarautun sun fito ne daga gidan sarautar Daura.

Muhimman Wurare a Tarihi:

· Kusurwar Daura: Wuri ne da aka ce  Bayajidda ya kashe maciji. Wuri ne mai tsarki da ake gudanar da bukukuwa a kai.

· Gidan Bayajidda: Gidan da aka gina a wurin da Bayajidda ya zauna kamar yadda wasu masana tarihi suka bayyana. Yana nan har yau a cikin birnin Daura, ya zama wajen ziyara ga masu yawon buɗe ido.

Sarauta: Daura tana da tsarin sarauta na gargajiya. Shugaban masarautar shi ne Sarkin Daura, amma a al'adance ana kiran sa da wani laƙabi mai daraja. A yau, Sarkin Daura na cikin manyan sarakunan jihar Katsina kuma yana da matsayi mai girma a cikin al'ummar Hausa.

Yau da Kullum: Masarautar Daura, duk da cewa ba ta da iko na siyasa kamar da, amma tana ci gaba da zama cibiyar al'adu, addini, da zamantakewa ga al'ummar Daura.

A taƙaice, wasu masanan sun bayyana Masarautar Daura a matsayin tushe da asalin al'ummar Hausa, kuma labarinta na Bayajidda da maciji ya zama labari wanda aka fi sani a matsayin asalin kafuwar Daura a doron duniya. Sai dai masana tarihi da dama sun musanta hakan.

Post a Comment

Previous Post Next Post