Rasha da China Sun Yi Veto Kan Kudirin Amurka a Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Ɗinkin Duniya — Rasha da China sun yi amfani da ƙuri’ar veto wajen dakile wani kudiri da Amurka ke mara wa baya a Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda zai ba ƙwararrun Majalisar damar ci gaba da sanya ido kan takunkuman da aka kakabawa Iran.

Kudirin da aka dakile a ranar Alhamis zai tsawaita wa’adin ƙwararrun masu zaman kansu da ke sa ido kan takunkuman da aka sake kakabawa Iran a bara, bayan da ƙasashen Yamma suka zarge ta da karya yarjejeniyar nukiliya ta shekarar 2015. Sai dai Tehran ta musanta cewa tana neman kera makamin nukiliya ko kuma ta karya yarjejeniyar.

Bayan kaɗa ƙuri’ar, Jakadan Rasha a Majalisar Ɗinkin Duniya, Vassily Nebenzia, ya buƙaci ƙasashen Yamma da su dakatar da abin da ya kira “matakai masu matuƙar haɗari” kan Iran, yana mai cewa hakan na iya ƙara dagula ƙoƙarin warware rikicin Tekun Farisa.

A shekarar 2025, Majalisar Tsaro ta sake kafa wani kwamiti mai zaman kansa na ƙwararru domin sanya ido da bayar da rahoto kan take dokokin takunkuman da aka kakabawa Iran, tare da ba da shawarwari kan matakan da za a ɗauka.

Sai dai ba a taɓa naɗa ƙwararrun cikin kwamitin ba saboda rashin jituwa tsakanin ƙasashe mambobin Majalisar Tsaron, lamarin da ya haifar da rashin daidaito kan batun.

A ranar Alhamis, ƙasashe 11 daga cikin mambobi 15 na Majalisar Tsaro sun kada ƙuri’ar amincewa da tsawaita wa’adin sa ido kan takunkuman Iran, yayin da Pakistan da Somalia suka kaurace wa kaɗa ƙuri’ar.

Ofishin Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya ya gode wa Rasha da China bisa adawa da kudirin Amurka, wanda Tehran ta bayyana a matsayin wani kudiri mai “manufar siyasa”.

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, Iran ta ce tana matuƙar godiya ga Rasha da China saboda “matsayinsu na ƙa’ida da daidaito”, tana mai cewa ƙasashen biyu sun hana Amurka da ƙawayenta yin amfani da Majalisar Tsaro domin cimma manufofinsu na siyasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post