Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cike da farin ciki game da ziyarar ban-girma da tsohuwar Uwargidan marigayi Shugaban Ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, ta kai masa.
ZlYa bayyana cewa, ziyara ce mai cike da mutunta juna, wadda kuma ta sake fito da muhimmancin nauyin da ke wuyan shugabanni wajen tabbatar da ci gaban ƙasa da jin daɗin al'umma.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na yanar gizo, Atiku Abubakar ya ja hankali a kan irin halin matsin lamba da iyalai ke fuskanta a faɗin Najeriya sakamakon hauhawar farashin man fetur, da abinci, da sufuri, da ilimi, da kiwon lafiya. Ya jaddada cewa yanayin da ake ciki a yanzu yana buƙatar matakai na ƙwarai domin sauƙaƙa wa jama'a nauyin rayuwa.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa 'yan Najeriya sun cancanci tattalin arziƙin da zai dawo musu da damammakin ci gaba, tare da tabbatar da cewa kowane gida yana gudanar da rayuwa cikin mutunci da wadatar zuci. A cewarsa, wannan ne irin tsarin ƙasar da ya kamata a gina tare. Najeriya ta zamo mai yi wa dukkan al'ummarta aiki ba tare da nuna bambanci ba.
Daga ƙarshe, Atiku ya jaddada buƙatar sake samar da fata nagari ga 'yan ƙasa da kuma yin gini na tattaunawa da haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki domin maida Najeriya wuri mai sauƙin rayuwa da wadatar arziƙi ga kowa.