Ƙungiyar Darika a Jihar Katsina ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, gabanin zaɓen 2027, tare da yin alkawarin ci gaba da mara wa jam’iyyar APC baya.
Mai Taimaka wa Gwamna Radda kan Harkokin Ɗarika, Malam Mahi Bello, ne ya jagoranci bayyana wannan matsaya a ranar Alhamis a Ameera Events Centre da ke Katsina, yayin wata addu’a ta musamman da aka shirya domin nuna goyon baya ga tafiyar siyasar Tinubu da Radda.
Shirin wanda Sheikh Dahiru Usman Bauchi Foundation da Maituraka Foundation suka shirya, ya kuma haɗa da rabon tallafin ƙarfafa tattalin arziƙi ga mata 500.
Da yake jawabi, Gwamna Radda ya bayyana shugabanci a matsayin amana da jama’a ke bai wa waɗanda suka zaɓa, yana mai cewa ya kamata shugabanni su kasance masu sanin nauyin da ke kansu.
Gwamnan ya buƙaci jama’a da su riƙa tantance gwamnatoci bisa manufofi, ayyuka da tasirin da ake iya gani, maimakon ra’ayoyin siyasa kawai. Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da ba da haɗin kai ga jami’an tsaro tare da sanar da su duk wani muhimmin bayani da zai taimaka wajen magance matsalar rashin tsaro.
Tsohon Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi kira ga malamai, shugabannin al’umma da masu kyawawan halaye da su ƙara shiga harkokin siyasa, yana mai cewa hakan na iya taimakawa wajen samar da shugabanci nagari.
Shi ma Sheikh Nasiru Dahiru Usman Bauchi, shugaban Sheikh Dahiru Usman Bauchi Foundation, ya yaba wa Gwamna Radda kan goyon bayan da yake bai wa al’umma, musamman a fannonin ilimi, matasa da ƙarfafa tattalin arziƙi.
Shugaban Maituraka Foundation, Abdulaziz Maituraka, ya sake tabbatar da goyon bayan gidauniyar ga gwamnatin jihar da jam’iyyar APC, tare da bayyana cewa za ta ci gaba da shirye-shiryen da ke tallafa wa mata, matasa da sauran al’umma.