Tinubu Ya Fara Aiwatar Da Aikin Tasoshin Kasuwancin Fasaha Na $500M, Domin Samar Wa Matasa Ayyukan Fasaha Na Ƙasa da Ƙasa
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aza harsashin aiwatar da tsarin Tasoshin Kasuwancin Fasaha na Zamani Mai 'Yanci (Digital Free Zones) a hukumance, inda ya ba da umarnin kammala tsarin gudanarwa a cikin kwana 180 domin jawo jarin ƙasashen waje, da daƙile ƙaurar ƙwararru, da kuma buɗe damar samun ayyuka masu tsada ga matasan Najeriya.
Wannan tsari yana da nufin sabunta dokokin wuraren kasuwanci masu 'yanci na Najeriya da aka ƙera sama da shekaru 30 da suka gabata, domin bai wa kamfanonin fasaha, kuɗi, da ayyuka na cikin gida damar samun jarin ƙasa da ƙasa da haɓaka kasuwancinsu, da riƙe haƙƙin mallakar fasaharsu a cikin gida ba tare da sun ƙaura zuwa ƙasashen waje ba.
Shugaba Tinubu ya umarci Ministar Kasuwanci da Zuba Jari, Dr. Jumoke Oduwole wadda ke matsayin Mataimakiyar Shugaba kuma Mai Haɗa Ayyukan Kwamitin Shugaban Ƙasa a kan Tasoshin Kasuwancin Fasaha da ta haɗa gwiwa da aikin ‘Itana Innovation’ domin kammala taswirar tafiyar da shirin.
Samar da ayyukan yi a faɗin ƙasa: An tsara shi ne domin ba wa matasa ƙwararru a birane irin su Kano, Enugu, Warri, Minna, Maiduguri, da Ibadan damar yin aiki kai tsaye ga kamfanonin ƙasa da ƙasa daga gida.
Tallafa Wa Ayyukan Ƙwararru: Baya ga ma'aikata da masana fasaha, tsarin zai haɗa da injiniyoyin masarrafan kwamfuta (software engineers), masu haɓaka shafuka, lauyoyi, akawu, da masu ƙira domin yi wa kamfanonin fasaha na ƙasa da ƙasa aiki.
Sabunta Dokoki da Tsare-tsare: Kwamitin gudanarwa na Shugaban Ƙasa zai sabunta tsarin da ya shafi harkar banki, haraji, shige da fice, sasanta taƙaddama, da kuma maida ayyukan gwamnati na na'ura mai ƙwaƙwalwa (digitization).
Babban ginshiƙin wannan shiri shi ne Itana, ta Farko ta Kasuwancin Fasaha Mai 'Yanci a Najeriya da Hukumar NEPZA ta ba wa lasisi. Tare da goyon bayan Hukumar Kuɗi ta Afirka (AFC), aikin na dalar Amurka miliyan 500 wanda yake a Alaro City, Lagos, ya haɗa cibiyar ƙirƙire-ƙirƙire tare da manufofi masu inganta kasuwanci domin haɓaka kasuwannin fasaha na Afirka a faɗin nahiyar.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa riƙe ribar tattalin arziƙi a cikin gida ya yi daidai da manufar gwamnatinsa ta 'Renewed Hope', sannan zai yi amfani da Yarjejeniyar Yin Ciniki Mai 'Yanci ta Afirka (AfCFTA) wajen sanya Najeriya ta zama babbar cibiyar fasaha a Afirka.