Tsohon fitaccen ɗan wasan tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles, Daniel Amokachi, ya kammala karatun horaswa tare da samun lasisin koyar da ƙwallon ƙafa na CAF A a ƙasar Morocco, lamarin da ya ƙara masa wani muhimmin mataki a fannin horaswa.
Amokachi, wanda aka fi sani da lakabin “The Bull”, ya sanar da samun wannan lasisi ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, inda ya bayyana godiyarsa ga Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Morocco saboda ba shi wannan dama.
A cikin saƙon nasa, Amokachi ya ce:
“A ƙarshe dai na samu lasisin CAF A. Ina godiya ga Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Morocco saboda wannan dama.”
Tsohon ɗan wasan na Najeriya ya riga ya yi aiki a matsayin mai horar da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Najeriya da kuma ƙasashen waje. Haka kuma, ya taɓa kasancewa cikin masu horas da tawagar Super Eagles a matsayin mataimakin koci.
Lasisi na CAF A yana daga cikin manyan takardun shaidar horas da ƙwallon ƙafa da Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ke bayarwa ƙarƙashin tsarin horas da masu koyar da ƙwallon ƙafa na nahiyar.
Samun wannan lasisi na nufin Amokachi ya ƙara wani muhimmin mataki a tafiyarsa ta horarwa, bayan shahararren tarihin da ya gina a matsayinsa na ɗan wasan ƙwallon ƙafa tare da Super Eagles da kuma sauran ƙungiyoyin da ya buga wa ƙwallo.