A wani rahoto da jaridar DW ta wallafa, ta bayyana cewa, akwai yiwuwar manyan jam'iyyun adawa da su haɗu wuri guda domin yaƙar babbar jam'iyya mai mulki wato APC.
Jaridar ta ruwaito cewa, jam'iyyun adawa a Najeriya na neman haɗin kan jagororin jam'iyyun ta hanyar ƙulla ƙawance, maimakon haɗuwa wuri guda, domin tsayar da ɗan takara ɗaya da zai ƙalubalanci jam'iyyar APC mai mulki a zaɓen da ke tafe.
A cewar sanarwar, ana sa ran jam'iyyun za su rattaɓa hannu kan yarjejeniyar ƙawance a mako mai zuwa.
Haka kuma, jaridar ta bayyana cewa, al'umma na ta tambayar irin tasirin da wannan ƙawance zai yi, duba da ƙalubalen da jam'iyyun adawar ke fuskanta, da kuma ƙarfin APC a matsayin jam'iyyar da ke kan mulki, wadda ta kafu sosai a jihohi da dama.