Gwamnatin Jihar Kano ta Biya Naira Biliyan 37 na Bashin 'Yan Fansho da ta Gada Daga Gwamnatin da ta Shude

Gwamnan Kano, ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa ta biya Naira biliyan 37 daga cikin bashin fansho da giratuti da ta gada daga gwamnatocin baya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin bikin sake biyan wasu tsofaffin ma’aikata da iyalan ma’aikatan gwamnati da suka rasu haƙƙoƙinsu a gidan gwamnatin Kano.

Ya ce gwamnatinsa ta fara sake biyan giratuti da alawus-alawus, inda wannan shi ne karo na bakwai da aka gudanar da irin wannan biyan kuɗi.

Abba ya tabbatar da cewa, gwamnatinsa za ta kammala biyan sauran bashin da ake bin ta kafin watan Afrilun 2027 mai zuwa.

Ya ce biyan kuɗaɗen na daga cikin ƙoƙarin gwamnatinsa na kula da jin daɗin ma’aikata, musamman waɗanda suka yi ritaya da kuma biyan iyalan waɗanda suka rasu.

A nasa ɓangaren, ƙungiyar tsofaffin ma’aikatan Najeriya (NUP) da ƙungiyoyin ƙwadago a jihar sun yaba wa gwamnatin bisa bayar da fifiko ga walwalar ma’aikata da waɗanda suka yi ritaya.

Ƙungiyar NUP ta kuma karrama gwamnan da lambar yabo ta gwamnan da ya fi kula da ma’aikata, bisa ƙoƙarinsa na biyan haƙƙoƙin ma’aikata da iyalan waɗanda suka rasu.

Post a Comment

Previous Post Next Post