Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Kebbi, na jihar Kebbi, domin halartar babban gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, yayin da dubban magoya bayan jam’iyyar suka taru domin tarbarsa.
Jirgin shugaban ƙasar ya sauka a filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello International Airport da misalin ƙarfe 11:44 na safe ranar Talata, inda Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, tare da takwarorinsa, ministoci da shugabannin jam’iyyar suka tarbe shi.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da matarsa sun isa filin jirgin tun da misalin ƙarfe 11:05 na safe, yayin da aka kuma ga jiragen sama masu zaman kansu guda 18 dauke da manyan baƙi.
Daga cikin waɗanda suka tarbi shugaban ƙasar akwai gwamnonin Kaduna, Uba Sani; Zamfara, Dauda Lawal; Yobe, Mai Mala Buni; Borno, Babagana Zulum; da Sokoto, Ahmad Aliyu.
Sauran sun haɗa da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda; Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Abdulaziz Yari; da Sanatoci Adams Oshiomhole da Ali Modu Sheriff.
Haka kuma, tsofaffin gwamnoni Ahmed Yerima, Ibrahim Shema da Abdullahi Ganduje sun halarci tarbar shugaban ƙasar.
Bayan isarsa, Tinubu ya nufi filin wasa na Haliru Abdu Multi-Purpose Stadium, inda aka gudanar da gangamin, tare da dubban magoya bayan APC da suka taru tun da misalin ƙarfe 7:00 na safe.
Magoya bayan, ciki har da mata da matasa, sun yi dafifi a kan titunan da ke kaiwa filin taron, suna kaɗa tutocin APC tare da ɗaga hotunan Tinubu da Gwamnan jihar Kebbi.
