Fayose Ya Zargi Obasanjo da Neman Tinubu Ya Taimaka wa ’Yarsa Ta Zama Gwamnan Ogun

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya zargi tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, da fara sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ne bayan ya gaza samun goyon bayanta kan burin ’yarsa, Iyabo Obasanjo, na zama gwamnan jihar Ogun.

Fayose

Fayose ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na TVC a ranar Litinin, inda ya ce Obasanjo ya nemi taimakon tsohon gwamnan Ogun, Olusegun Osoba, domin ya shawo kan Tinubu ya goyi bayan takarar ’yarsa.

A cewarsa, hakan ne ya sa Obasanjo ya tarbi Tinubu lokacin da ya kai ziyara jihar Ogun a watan Afrilun 2026 domin ƙaddamar da filin jirgin saman Gateway International Cargo Airport.

Fayose ya ce bayan yunƙurin bai yi nasara ba, Obasanjo ya sauya matsayinsa, inda ya koma sukar gwamnatin Tinubu.

Ya kuma bayyana tsohon shugaban ƙasar a matsayin mutumin da ba ya ganin alherin wasu shugabanni, yana mai cewa a baya ya sha sukar gwamnatocin marigayi Umaru Musa Yar’Adua da Goodluck Jonathan.

Sai dai Iyabo Obasanjo, wadda ta nuna sha'awarta ta neman takarar gwamnan  a ƙarƙashin jam’iyyar APC a watan Fabrairun 2026, ta dakatar da burinta bayan jam’iyyar ta amince da Sanata Solomon Adeola a matsayin ɗan takararta na maslaha.

Ana dai samun saɓani tsakanin Fayose da Obasanjo, inda suke musayar zarge-zarge da kalamai masu zafi a kafafen yaɗa labarai tsawon shekaru.

Post a Comment

Previous Post Next Post