Ministan Babban Birnin Tarayyar Najeriya (FCT), Nyesom Wike, ya amince da ɗaga muƙamin malamai 4,220 da kuma wasu ma’aikatan gwamnati 3,494, bayan kammala atisayen ɗaga muƙami na shekarun 2025 da 2026 da Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin FCT ta gudanar.Shugaban Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin FCT, Emeka Ezeh, wanda ya sanar da amincewar a ranar Talata, ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin FCT ƙarƙashin jagorancin Wike na ƙara wa ma’aikata ƙwarin gwiwar gudanar da ayyukansu.
A cewar Ezeh, Ministan FCT ya umarci hukumar da ta biya dukkan basussukan ɗaga muƙamin ma’aikata da aka gada daga tsohuwar gwamnati, tare da tabbatar da cewa an ɗaga muƙamin duk ma’aikatan da suka cancanta.
Ya ce: “Kamar yadda za ku iya tunawa, Ministan ya amince da yafewa jami’an ilimi da suka kawo cikas ga atisayen ɗaga muƙami na shekarar 2025, tare da ba su damar shiga atisayen shekarar 2026.
“Daga bisani, hukumar ta gayyaci dukkan jami’an ilimi da suka cancanci shiga atisayen ɗaga muƙami na shekarun 2025 da 2026 domin su halarci atisayen da aka kammala kwanan nan.”
Ezeh ya taya ma’aikatan da suka samu nasarar ɗaga muƙami murna, tare da buƙatar sauran ma’aikata da su rama wannan karamci ta hanyar gudanar da ayyukansu bisa ƙwazo da himma.
Shugaban hukumar ya kuma bayyana cewa hukumar za ta gudanar da taronta na biyu na shirya ma’aikatan FCTA masu shirin yin ritaya, waɗanda za su yi ritaya tsakanin ranar 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Maris na shekarar 2027.
Ya ce an tsara gudanar da taron ne a ranar 16 ga watan Disamba, 2026, domin shirya ma’aikatan da za su yi ritaya yadda za su tunkari rayuwa bayan barin aikin gwamnati.
Ana sa ran ma’aikatan FCTA guda 116 za su yi ritaya a zangon farko na shekarar 2027.
A watan Yulin 2026, Wike ya amince da ɗaga muƙamin ma’aikatan gwamnati 3,592, bayan kammala atisayen ɗaga muƙami na shekarar 2025 da Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnati ta gudanar.