Gwamnatin Birtaniya ta ƙaƙabawa kamfanonin gine-gine takwas na Isra'ila takunkumi saboda zargin hannu wajen ayyukan gine-gine da faɗaɗa matsugunan Yahudawa a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan (West Bank) da Isra'ila ta mamaye.
Matakin na daga cikin ƙoƙarin Birtaniya na matsa wa Isra'ila lamba kan ayyukan matsugunan Yahudawa da take ci gaba da faɗaɗawa a yankin Falasɗinu, wanda ƙasashen duniya da dama ke kallon sa a matsayin abin da ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.
Takunkuman na iya shafar harkokin kuɗi da kasuwanci na kamfanonin da abin ya shafa, tare da takaita damar gudanar da wasu muhimman ayyukansu a ƙarƙashin dokokin Birtaniya.
Birtaniya ta sha bayyana adawarta da faɗaɗa matsugunan Yahudawa a yankunan Falasɗinu da Isra'ila ta mamaye, tana mai cewa irin waɗannan ayyuka na kawo cikas ga samar da zaman lafiya da kuma cimma mafita ta ƙasashe biyu, wato Isra'ila da Falasɗinu su zauna a matsayin ƙasashe masu cin gashin kansu.
Matakin na zuwa ne yayin da matsin lamba kan Isra'ila ke ƙaruwa daga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, saboda rikicin Falasɗinu da Isra'ila da kuma yadda ake ci gaba da samun rahotannin cin zarafin Falasɗinawa a yankunan da aka mamaye.
