Shugaban 'yan adawar ƙasar Mozambique, Venâncio Mondlane, ya gurfana a gaban Kotun Ƙoli ta ƙasar domin fuskantar shari'a kan zargin hannu a zanga-zangar da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama bayan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2024.
Mondlane na fuskantar tuhume-tuhume guda biyar, ciki har da tunzura mutane wajen aikata ta'addanci da kuma tayar da hankalin jama'a domin bijirewa dokoki. Idan aka same shi da laifin mafi girman tuhumar, zai iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 24 a gidan yari. Sai dai ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa, yana mai cewa shari'ar na da nasaba da siyasa.
Rikicin ya samo asali ne bayan zaɓen shugaban ƙasa na watan Oktoban 2024, inda Mondlane ya zo na biyu a bayan Daniel Chapo na jam'iyyar Frelimo mai mulki. Mondlane ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓen, yana zargin an tafka maguɗi. Wannan ya sa ya yi kira ga magoya bayansa da su gudanar da zanga-zanga tare da kaurace wa ayyukan yau da kullum.
Zanga-zangar ta ɗauki tsawon watanni, inda ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa sama da mutane 300 ne suka mutu, bisa bayanan ƙungiyoyin sa ido na cikin gida. Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun kuma zargi jami'an tsaro da amfani da ƙarfin da ya wuce kima wajen tarwatsa masu zanga-zangar.
Kafin fara shari'ar, an girke jami'an tsaro da dama a hanyoyin da suka nufi Kotun Ƙoli da ke birnin Maputo, yayin da wasu magoya bayan Mondlane suka taru a wajen kotun domin nuna goyon bayansu gare shi. Mondlane ya bayyana cewa yana cikin kwanciyar hankali kuma yana da kwarin gwiwa kan lauyoyinsa.
A nasa ɓangaren, jam'iyyar Mondlane ta bayyana shari'ar a matsayin wani yunƙuri na siyasa domin murƙushe 'yan adawa. Sai dai shugaban Kotun Ƙoli ya musanta zargin cewa ana yi wa shari'ar katsalandan na siyasa, yana mai cewa kotu za ta yi hukunci bisa doka.
Ana sa ran shari'ar za ta ɗauki watanni ana gudanar da ita, yayin da ake ci gaba da sanya ido kan yadda za ta gudana da kuma tasirinta ga siyasar Mozambique.
