Ɗan ƙwallon duniya na shekarar 2008 Cristiano Ronaldo ya sanar da ritayarsa daga tawagar ƙasar Portugal bayan shafe shekaru 23 yana wakiltar ƙasar.
Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya, Cristiano Ronaldo, ya sanar da ritayarsa daga buga wa tawagar ƙasar Portugal wasa, bayan shafe shekaru 23 yana wakiltar ƙasar.
Ronaldo mai shekaru 41 ya bayyana cewa lokaci ya yi da zai ajiye rigar ƙasar mai lamba bakwai, domin bai wa matasa 'yan wasa damar ci gaba da wakiltar Portugal.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Ronaldo ya ce matakin ya kasance mai sosa rai, amma ya gode wa iyalinsa da magoya baya da duk waɗanda suka taka rawa a tafiyar tasa.
Ronaldo ya fara bugawa Portugal wasa a shekarar 2003, inda ya buga wasanni 234 tare da zura ƙwallaye 146, abin da ya sa ya zama ɗan wasan da ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihin ƙasashen duniya.
Ya kuma taimaka wa Portugal lashe gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2016, da kuma gasar Nations League a shekarun 2019 da 2025.