Hukumar ACRESAL ta fara shirye-shiryen gina babbar magudanan ruwa a garin Kankia bayan da ES KASAMA Lawal Aminu Bala PhD ya shigar da neman hakan gare ta
Hukumar ACRESAL ta fara duba yiwuwar gudanar da babbar magudanan ruwa irin wadda ta yi a Katsina amma a garin Kankia, a ƙoramar Inchimamu a wani yunƙuri na magance ambaliyar ruwa da zaizayar ƙasa.
Tawagar ACRESAL ta turo da Ma'aikatan ta don duba wa, bayan da Shugaban Hukumar kula da kadarorin Gwamnatin Jihar Katsina kuma jigo kuma ɗaya daga cikin masu ruwa da tsakin Kankia Lawal Aminu Bala PhD ya shigar da buƙatar yin hakan kai tsaye ga shugabanta.
Hukumar ta bayyana cewa, aikin zai taso ne daga Sabuwar duniya ya ratsa zuwa Zango, bayan sabon birni da Ƙofar Yamma da layi da unguwar rinji har zuwa Dam. Za a gina sabuwar gasar ne domin magance matsalar ambaliyar ruwa tare da kare dukiyoyi da rayukan al'umma tare da bunƙasa ci gaban garin Kankiya, da tattalin arziƙinta.
Injiniyoyin daga ACRESAL da suka duba aiki akwai Injiniya Salisu Sulaiman da yake Project Engineer da Abdulwahab Ibrahim wanda shi ne livelihood officer.
Tun da farko tawagar hukumar sun fara sauka ne a gidan Hakimin garin Kankia Alhaji Musa Hassan Sada, domin shaida mashi dalilin zuwansu, domin ɗaukar zane da duba yanayin yadda ƙoramar take.