Wike Ya Yi Watsi da Barazanar Yajin Aikin ASUU Kan Ƙwace Filin Jami’ar Abuja

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi watsi da barazanar shiga yajin aikin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Abuja (UniAbuja), ta yi kan sake ware wasu sassan filin jami’ar ga kamfanoni masu zaman kansu da hukumomin gwamnati.Da yake mayar da martani a ranar Alhamis, yayin tattaunawarsa da manema labarai na wata-wata a Fatakwal, bayan barazanar ƙungiyar ta shiga yajin aiki, Wike ya nuna shakku kan hurumin ASUU na tsoma baki a harkokin rabon filaye da doka ta tanada, yana mai cewa ƙungiyoyin ƙwadago ba su da hurumi ko ikon kula da harkokin filaye a babban birnin ƙasar.

Wike ya ƙi amincewa da zargin ƙungiyar na cewa gwamnati na ƙwace filayen jami’ar ba bisa ƙa’ida ba, inda ya ce mallakar filaye da tabbatar da bin tsarin gine-gine na babban birnin tarayya na ƙarƙashin ikon Hukumar Gudanar da Babban Birnin Tarayya (FCTA).

“Me ya haɗa ASUU da filayenmu? Ta yaya ASUU za ta zama mamallakiyar fili? Shin ASUU ce ta mallaki ƙungiyar a Najeriya yanzu? Shin wannan haƙƙin ƙungiyar ne?” Wike ya tambaya.

Da yake magana kan takaddamar filin jami’ar, wanda rahotanni suka ce ya kai sama da hekta 11,000, ministan ya nuna rashin dacewar jami’a guda ta mallaki faɗin filaye masu yawa da ba a bunƙasa ba, tare da hana ayyukan raya ƙasa.

Ya jaddada cewa matakan da FCTA ke ɗauka ci gaba ne da aiwatar da manufofin gwamnati da kuma tsarin tsara birane.

Dangane da sanarwar ASUU na cewa za ta shiga yajin aiki tare da ƙalubalantar matakin FCTA a kotu, Wike ya ce gwamnatin ba ta damu da barazanar shari’a ko ta yajin aiki ba.

Ya bayyana cewa idan ƙungiyar ta zaɓi zuwa kotu domin neman hakkinta, FCTA a shirye take ta kare haƙƙoƙinta na kundin tsarin mulki da kuma nauyin da doka ta ɗora mata.

Ministan ya kuma soki shugabannin ƙungiyar bisa amfani da barazanar yajin aiki a matsayin hanyar matsa wa gwamnati lamba, inda ya buƙace su da su mutunta ƙa’idojin aikin gwamnati, maimakon yunƙurin yin amfani da barazana wajen tilasta wa gwamnati amincewa da buƙatunsu.

Wike ya sake jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da matakan dawo da filayen da ba a amfani da su, yana mai cewa cibiyoyin gwamnatin tarayya ba za su iya killace dubban hekta ba tare da cikakkun takardun mallaka, izini da kuma amfani da su yadda ya kamata ba.

Wannan takaddama ta biyo bayan wani taron manema labarai da shugaban ASUU na Jami’ar Abuja, Dakta Sylvanus Ugoh, ya gudanar kwanan nan, inda ya yi gargaɗin cewa ƙungiyar ba za ta iya ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a jami’ar ba idan ministan FCT ya ƙi janye rabon filayen da aka ware daga yankin da aka tanadar wa jami’ar a gundumar Giri.

ASUU ta bayyana cewa hekta 11,824 da aka ware wa jami’ar tun farko suna da matuƙar muhimmanci wajen faɗaɗa jami’ar nan gaba, gudanar da binciken aikin gona da kuma samar da muhimman ababen more rayuwa.

Sai dai Wike ya sake nanata cewa FCTA ba za ta amince da duk wani yunƙurin matsa mata lamba ta hanyar barazana ba, yana mai cewa duk wani rabon fili a cikin babban birnin tarayya yana ƙarƙashin kulawar ofishinsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post