Hukumar Shirya Zabe ta Kasa INEC ta Sanar da Dalilin da ya sa Suka Kara Yawan Rumfnunan Zabe

Hukumar shirya zaɓe ta ƙasa INEC ta ce ƙarin da aka samu na wasu rumfunan zaɓe sun samo asali ne daga hukuncin da kotu ta yanke, wanda ya haifar da ƙirƙirar sabbin mazaɓu a jihohin Kogi da Benue da kuma Delta.

Wannan na zuwa ne bayan ɓullar wasu rahotanni da ke nuna cewa, hukumar ta ƙara rumfunan zaɓe 453, inda adadinsu ya tashi daga 176,846 zuwa 177,299.

Sai dai har zuwa yanzu, hukumar INEC ba ta tabbatar da wannan ƙarin adadin rumfnunan ba, amma ta bayyana cewa, za ta yi wa masu ruwa da tsaki cikakken bayanin yadda al'amarin yake bayan kammala bincikenta.

Haka kuma, hukumar na ci gaba da fukantar tambayoyi kan zargin amfani da hotunan bogi da aka ƙirƙira da fasahar AI a wasu daga cikin rajistar masu zaɓe.

Post a Comment

Previous Post Next Post