Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da kammala aikin gina babbar tashar motocin fasinjoji ta Kakuri, wadda aka fi sani da Southern Terminal, a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani.
Sabuwar tashar ta ƙunshi manyan wuraren hawa da sauka guda huɗu, waɗanda aka tsara domin amfanin fasinjoji da ƙungiyoyin masu sufuri.
Haka kuma, tashar tana da masaukin baƙi da gidajen cin abinci haɗi da shaguna siyayya da kuma ofisoshin gudanarwa tare da tashar kashe gobara, baya ga wasu muhimman kayayyakin more rayuwa.
Bayan kammala tashar ta Kakuri an samu ƙarin yawaitar cibiyoyin sufuri na zamani a jihar Kaduna, tare da tashar motoci tsakanin jihohi da ke Millennium City da kuma tashar Sobawa da ke Rigachikun.
Gwamnatin ta ce ana sa ran waɗannan ayyuka za su taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirgar fasinjoji da inganta harkokin sufuri da kuma samar da ingantaccen tsarin sufurin jama'a a faɗin jihar.
Kamfanin Standwell Structures Nigeria Limited ne ya gudanar da aikin, ƙarƙashin kulawar Hukumar Kula da Zirga-zirgar Sufuri ta Jihar Kaduna (KADSTRA).
Gwamnatin ta bayyana cewa, kammala tashar na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na zamanantar da harkokin sufuri da inganta ayyukan da ake samarwa fasinjoji.