Romelu Lukaku ya yi ritaya daga buga wa Belgium wasanni, yana mai cewa ya "ji daɗin kowane lokaci" da ya shafe yana wakiltar kasar.
Dan wasan mai taka leda a Fenerbahce mai shekara 33 ya fara buga wa Belgium wasa a shekarar 2010, kuma shi ne wanda ya fi kowa cin ƙwallaye a tarihin tawagar ƙasar da 94 a raga a wasa135.Shi ne na biyar cikin masu yawan cin ƙwallaye a wasannin ƙasa da ƙasa a duniya a tarihi, bayan Sunil Chhetri, Ali Daei, Lionel Messi da kuma jagora Cristiano Ronaldo, wanda ya ci ƙwallaye 146.
Lukaku ya ci ƙwallaye takwas a gasar kofin duniya guda huɗu da ya halarta, ciki har da lokacin da Belgium ta kai wasan kwata-fainal a gasar bana, sannan ya ci jimillar ƙwallaye shida a gasar European Championship guda uku.