Dukkan majalisun dokokin jihohi 36 na Najeriya sun amince da ƙudirin kafa rundunar ’yan sandan jihohi, a ƙarƙashin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar na 1999 karo na shida da ake ci gaba da yi.Magatakardan Majalisar Dokokin Tarayya, Barrister Kamoru Ogunlana, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa wakilan majalisar a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa a shirye yake ya miƙa ƙudirin ga Shugaban Ƙasa domin amincewarsa, bayan kammala aikin tantance takardun a ofishinsa.
Ya ce: “Magatakardan Majalisar Dokokin Tarayya na sanar da cewa dukkan majalisun dokokin jihohi 36 sun amince da ƙudirin dokar gyara kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na 1999, domin samar da rundunar ’yan sandan jihohi da sauran abubuwan da suka shafi hakan.”
Ya ƙara da cewa amincewar ta nuna cewa kashi 100 cikin 100 na majalisun dokokin jihohin sun goyi bayan ƙudirin, adadin da ya haura mafi ƙarancin jihohi 24 da sashe na 9(2) na kundin tsarin mulkin ƙasar, kamar yadda aka yi wa gyara, ya tanada.
Ogunlana ya ce yana da muhimmanci a fahimci cewa ƙudirin ya daɗe da cika dukkan ƙa’idojin kundin tsarin mulki da na gudanarwa da ake buƙata kafin miƙa shi, kamar yadda kundin tsarin mulki da dokar tabbatar da sahihancin dokoki ta shekarar 2004 suka tanada.
Sai dai ya bayyana cewa shugabannin Majalisar Dokokin Tarayya sun bayar da umarnin ɗan jinkiri wajen miƙa ƙudirin domin ba da damar samun ƙarin fahimtar juna a matakin ƙasa da kuma tattaunawa da dukkan jihohin tarayyar.
Ya ce amincewar bai-ɗaya da aka samu kan ƙudirin wani babban ci gaba ne da ba a taɓa ganin irinsa ba, wanda ke nuna kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin Majalisar Dokokin Tarayya da majalisun dokokin jihohi, da kuma haɗin kai tsakanin ɓangarorin zartarwa na gwamnatin tarayya da na jihohi.
Magatakardan ya ƙara da cewa bayan kammala aikin tantance takardun a ofishinsa, an shirya miƙa ƙudirin ga Shugaban Ƙasa domin samun amincewarsa.
A cewarsa, wannan nasara za ta zama tubalin da zai taimaka wa Majalisar Dokokin Tarayya wajen kammala sauran ƙudirorin gyaran kundin tsarin mulki karo na shida da kuma miƙa su ga majalisun dokokin jihohi domin su yi nazari a kansu cikin gaggawa.
A ƙarshe, Ogunlana ya ce shugabanni da mambobin Majalisar Dokokin Tarayya sun yaba wa gwamnonin jihohi 36, shugabanni da mambobin majalisun dokokin jihohi, da sauran masu ruwa da tsaki bisa haɗin kai da jajircewarsu wajen yin garambawul ga tsarin aikin ’yan sanda a Najeriya.