Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya ce gwamnatin Amurka ba za ta bari yaƙin da take yi da Iran ya ɗauki tsawon shekara biyu ba.
Ya kuma jaddada cewa shirin nukiliyar Iran na ci gaba da zama barazana ga Amurka."Mun yi wa al'ummar Amurka alƙawarin cewa ba za mu sake shiga yaƙe-yaƙen da ba su da iyaka ba," in ji Vance a wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai ta Fox News ranar Litinin.
"Haƙiƙa shugaban ƙasa ya yi imanin cewa dole ne a lalata shirin nukiliyar Iran, kuma gaskiya ne cewa wannan shiri barazana ne ga Amurka. Amma ba za mu bari wannan rikici ya rikiɗe ya zama yaƙin da zai ɗauki shekara 10 ko 15 ba, ko ma shekara biyu," in ji shi.
Kalaman Vance na nuni ne ga shekaru biyun da suka rage wa wa'adin mulki na biyu na Trump.