Wace AI ce ta zama Minista a Albaniya?
Gwamnatin Firayim Minista Edi Rama ta gabatar da wata fasahar AI mai suna “Diella”, kalma da a harshen Albaniya ke nufin “Rana.” An gabatar da ita a matsayin mamba a gwamnatin ƙasar, ba wai mutum ba amma an ƙirƙire ta ta hanyar fasahar ƙere-ƙere.
Ayyukanta na farko sun shafi
kulawa da harkokin saye da sayarwa da kwangilolin gwamnati, domin tabbatar da
cewa ana gudanar da su cikin gaskiya, ba tare da cin hanci da rashawa ba. 🕵️
A cewar Firayim Ministan, dalilin
naɗin Diella shi ne
magance cin hanci da rashawa da ya daɗe
yana damun ƙasar,
matakin da zai taimaka wajen shigar Albaniya cikin Tarayyar Turai (EU).
An nuna Diella a matsayin mace
sanye da kayan gargajiya na Albaniya, inda za ta yi amfani da bayanan “data,”
bincike, da algorithms wajen gudanar da ayyukanta.
Tambayoyi ga masu karatu
Wace rawa kuke ganin Diella za ta
taka a gwamnatin Albaniya?
Shin AI za ta iya magance cin
hanci da rashawa a zahiri?
Ku bayyana ra’ayoyinku a nan! 💬
