Aitana Bonmatí, ‘yar ƙungiyar Barcelona da ‘yan ƙasar Sifaniya, ta sake lashe kyautar Women’s Ballon d’Or na 2025 - wannan shi ne karo na uku a jere (2023, 2024, 2025).
Ta samu nasarar ne duk da ƙalubale,
yayin da Barcelona suka yi Domestic treble, kuma sun kai ƙarshe
a gasar Champions League ta mata, inda suka yi rashin nasara da Arsenal da ci
1-0.
Bonmatí ta taka rawa mai muhimmanci a gasar EURO 2025 na mata don ƙasar Sifaniya, ciki har da zura ƙwallo a lokacin da aka ci gaba da wasan mintuna na ƙari (extra time) a ragar ƙarshe.
