Tauraron tsohon ɗan wasan kwallon kafa, Ronaldinho, ya miƙa kyautar Ballon d’Or a hannun Ousmane Dembélé, mai shekara 28. Dembélé, wanda ke taka leda a ƙungiyar PSG ta ƙasar Faransa, shi ne ya lashe kambun zama Ɗan Kwallon Duniya na Shekarar 2025.
Ya karɓi kambun ne daga hannun Rodri, ɗan wasan tsakiya na Manchester City, haifaffen ƙasar Sifaniya.
Dembélé ya samu wannan nasarar ne bayan ya zura ƙwallaye 37 tare da bayar da tallafin 17 a cikin wasanni 60 da ya buga a kakar da ta gabata. Haka kuma ya jagoranci ƙungiyarsa wajen lashe kofuna biyar a jere, waɗanda suka haɗa da Ligue 1 da Champions League.
Lamine Yamal ya zo na biyu, yayin da Raphinha ya zo na uku - dukkansu suna taka leda a ƙungiyar Barcelona ta ƙasar Sifaniya.
