Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ya nemi a kafa tsarin diflomasiyyar majalisa domin ƙarfafa hulɗar Najeriya da Kyuba a fannoni da suka haɗa da kiwon lafiya, ilimi, bincike da kuma zuba jari na musamman.
Abbas ya yi wannan kira ne a Abuja
yayin da ya karɓi tawagar ƙasar Kyuba ƙarƙashin jagorancin Hon. Fernando
González Llort, fitacce a ƙasar kuma shugaban Cibiyar Abokantaka ta
Kyuba (ICAP). Kakakin, wanda Mataimakinsa, Hon. Benjamin Kalu, ya
wakilta, ya bayyana cewa akwai buƙatar zurfafa dangantaka tsakanin ƙasashen
biyu.
Ya lissafo muhimman fannoni da za a
yi aiki a kai, ciki har da diflomasiyyar majalisa, kiwon lafiya, kasuwanci da
al’adu, kimiyyar halittu da masana’antar magunguna.
Abbas ya ce hukumar Abokantakar
Majalisar Najeriya da ta Kyuba za ta zama hanyar samar da yarjejeniyoyi,
amincewar majalisa, da shirye-shiryen da za su haifar da sakamako kai tsaye. Ya
ƙara da cewa akwai buƙatar a juya kusanci na al’adu da ake da shi a waƙa,
wasanni da adabi zuwa damar kasuwanci ga ’yan Najeriya.
A ɓangaren kiwon lafiya, Kakakin ya
yaba da rawar da Kyuba ta taka wajen tura likitoci zuwa ƙasashe daban-daban,
yana mai cewa haɗin gwiwa a horaswa da samar da magunguna da rigakafi zai
taimaka wajen ƙarfafa tsarin lafiya a Najeriya.
Shugaban tawagar Kyuba, Fernando
González Llort, ya yaba da dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu, yana
mai cewa akwai buƙatar ƙarfafa musayar ziyara da haɗin kai tsakanin majalisun
dokokin Najeriya da na Kyuba. Ya kuma bayyana sha’awar ƙasarsa na ƙara hulɗa da
Najeriya a fannin tattalin arziƙi.
Llort ya miƙa gayyata ga Mataimakin
Kakakin Majalisar Najeriya domin ziyartar Kyuba, inda za a ci gaba da
tattaunawa kan diflomasiyyar majalisa da sauran fannoni na moriyar juna.
