Shahararren ɗan kasuwa kuma mafi arziki a Afirka, Aliko Dangote, ya zargi Ƙungiyar Ma’aikatan Dakon Mai da Gas na Najeriya (NUPENG) da ɗora kuɗaɗe har ₦50,000 a kan kowace babbar mota da ke ɗaukar man fetur daga sabuwar matatar man fetur ɗinsa.
Dangote ya bayyana haka ne a yayin
da yake mayar da martani kan ƙorafin NUPENG cewa kamfaninsa na hanawa direbobin
motocin CNG guda 4,000 da ya ƙaddamar shiga ƙungiya.
“Ina gaya muku gaskiya: kowace mota
da za ta ɗauki mai daga nan, NUPENG na karɓar kusan ₦48,000 zuwa ₦50,000.
Idan kuma wasu masu ruwa da tsaki suka ƙara nasu, kuɗin zai kai ₦80,000
zuwa ₦84,000. To wa zai biya wannan kuɗi? A ƙarshe, jama’a ne za su sha
wahala,” in ji shi.
Ya ce irin waɗannan kuɗaɗen
“rent-seeking” ne - wato cin moriya ba tare da wani aiki ba - wanda ke rage
inganci a harkar rarraba mai. Dangote ya kuma tuna yadda a da, lokacin da yake
shigo da man fetur daga waje, masu sufuri suka shaƙe masa rai, abin da ya sa
daga baya ya samar da motocin sufuri nasa ƙarƙashin kulawar ɗan’uwansa.
“Yanzu da muka fito da motocin CNG
ɗinmu, ba za mu bari a sake riƙe mu da garkuwa ba. Idan babu jigilar mai, babu
abin da za mu iya yi,” in ji shi.
Dangote ya jaddada cewa, ko da yake
ya amince ma’aikata na da ’yancin shiga ƙungiya, bai kamata a tilasta wa kowa
ba. “Ko addini ma zaɓi ne; ba za ka tilasta wa kowa ya sauya akida ba,” in ji
shi.
Saɓanin haka, lokacin da aka nemi
jin ta bakin Shugaban NUPENG, Comrade Williams Akporeha, bai tabbatar da
zargin ba, bai kuma karyata shi gaba ɗaya ba. A maimakon haka ya mayar da
martani cikin zolaya: “₦50,000 yanzu? Ashe ba ₦1 a kowace lita ba ne?”
Tun a baya dai, yayin da ake ta
maganganu a kafafen sada zumunta cewa ƙungiyar na karɓar ₦1 a kowace lita,
Akporeha ya ce: “Ba za ka hana mutane su faɗi ra’ayinsu ba. Amma duk wanda ya
yi zargi, sai ya gabatar da hujja.”
Masana harkar man fetur sun nuna damuwa kan yadda ƙungiya za ta zama tamkar mai karɓar haraji, suna mai gargadin cewa hakan zai ƙara tsadar man fetur a tashoshi, alhali mutane ke ci gaba da fama da tsadar rayuwa a ƙasar.
