Barcelona na zawarcin kaftin ɗin Ingila, Harry Kane, mai shekara 32, wanda ya zura ƙwallaye 95 a wasanni 102 da ya buga wa Bayern Munich a gasar lig da kuma kofin duniya. Ana kallon Kane a matsayin wanda ya dace ya maye gurbin ɗan wasan gaba na Barça, ɗan ƙasar Poland Robert Lewandowski, mai shekaru 37. (El Nacional)
Za a bai wa kocin Manchester United,
Ruben Amorim, kuɗi domin neman ɗan wasan Nottingham Forest na Ingila, Elliot
Anderson, mai shekara 22, a watan Janairu. (Teamtalk)
Chelsea, Manchester United da
Newcastle United duk suna zawarcin ɗan wasan tsakiya na Real Madrid ɗan ƙasar
Faransa, Eduardo Camavinga, mai shekara 22, wanda farashinsa ya kai Yuro
miliyan 80.
Tags
Wasanni