Anya Super Eagles Za Su Kai Bantensu

Ƙungiyar ƙwallon ƙafar Super Eagle ta Nijeriya za su iya samun gurbin wasan cin kofin duniya idan suka cinye sauran wasanninsu biyu da suka rage masu. Wasannin za su gudana ne tsakaninsu da Lesotho a kasar Lesotho da kuma Benin wanda za a yi shi a gida Nijeriya. 
Wannan karsashi ya samu ne bayan da aka kama ƙungiyar ƙwallon ƙafar South Africa da laifin karya wata doka a wasanta da Lesotho, wanda hakan ya sa aka ci ta tarar kuɗaɗe da kuma rage mata maki uku. Hakan ya sa South Africa wadda ke jagorantar rukunin da maki 17 ta dawo a matsayin ta biyu da maki 14 da ƙwallaye 3, yayin da ƙungiyar ƙwallon ƙafar Benin ke jagorantar rukunin a yanzu da maki 14 da kuma ƙwallaye 4, sai kuma Nijeriya da ke take wa South Africa baya a matsayin ta uku da maki 11 da ƙwallaye 2, sai Rwanda da take matsayin na 4 da maki 11 babu ƙwallo ko guda.
Kuna ganin Nijeriya za ta kai bantenta kuwa?

Post a Comment

Previous Post Next Post