Harry Kane Ya Kafa Sabon Tarihi

Tsohon ɗan ƙwallon ƙungiyar Tottenham wanda yanzu haka yake taka leda a ƙungiyar Bayern Munich da take a ƙasar Jamus, ya kafa sabon tarihi, inda ya shafe tarihin Haland da Ronaldo na cin ƙwallaye ɗari (100) dukkansu a wasanni 105.
Harry Kane ɗan kwallon gaban Ingila ya kafa sabon tarihi, inda ya zama mutum na farko da ya fi kowa saurin zura ƙwallaye ɗari (100) a cikin ƙasashen Turai 5 da suke buga ƙwallo. Ya samu wannan nasarar ne ta cin ƙwallo 100 a wasanni (104) da ya buga tare da bayar da taimakon zura ƙwallo (assist)
Hoton Harry Kane
29.
Ɗan wasan ya kafa tarihin ne bayan da ya zura ƙwallaye biyu yau a wasansu da Werder Bremen a wasan cin kofin Bundeliga na Jamus.

Post a Comment

Previous Post Next Post