Da Kuri'ar Barawo Da Ta Liman Duk Darajarsu Daya

A firar da jaridar BBC ta yi da shi a jiya Alhamis, tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon shugaban jam'iyar APC mai mulki, ya bayyana cewa, 'Da ƙuri'ar ɓarawo da ta liman duk darajarsu ɗaya.' ya bayyana haka ne, a taron masu faɗa a ji na jam'iyyar APC ta jihar Kano da suka shirya, ya ce sun gudanar da taron ne domin su ga irin ci gaban da suka samu.

Ya kuma, ce su a jam'iyyarsu ta APC ba za su rufe ƙofa ba duk wanda yake son shigowa jam'iyar za su yi mashi lalle su yi masa joɓɓama. Sai dai za su kira su da masu yin amai su lashe, sannan su jam'iyyarsu ta APC tana da tsari da dokokin mulki da ya wajaba a bi.

A firar ta su ya ambaci ficewar sakataren gwamnatin Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP zuwa APC a matsayin wata babbar nasara da suka samu.

Ya ƙara da cewa, alaƙarsa da shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu tana nan kamar yadda take ko ma a ce ta fi da, ajiye muƙaminsa na shugaban jam'iyyar ba shi da nasaba da wani abu da zai kawo tasgaro ko cikas a tsakaninsu, domin wani abu ne na doka ko tsari da aka bi.

Abin tambayar a nan, WANE NE ƁARAWON WANE NE KUMA LIMAN? ku ajiye mana amsar a ɓangaren kwament.

Post a Comment

Previous Post Next Post