An Haifi Jaririya Da Kai Daya Da Idanu Biyu

Allah gwanin hikima, a yau ne muka samu labarin an kai wata mata mai juna biyu asibitin Ali Ƙwara da ke Azare ta jihar Bauchi. 
Matar ta kasa haihuwa har sai da ta kai an yi mata aiki. Bayan an yi wa mahaifiyar tiyata an ciro yaron, sai aka ganshi da kai ɗaya da fuska biyu da baki biyu da kunnuwa huɗu da kuma hanci biyu. 
Allah gwanin hikima. Muna addu'ar Allah ya ba wa mahaifiyar lafiya ya kuma raya yaron.

Post a Comment

Previous Post Next Post