An Shirya Muƙabala Kan Batun Batanci Da Ake Zargin Triumph Da Aikatawa

Majalisar Shura ta jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin sakataren majalisar kuma Kwamishinan kasuwanci na Kano Alhaji Shehu Wada Sagagi ya tabbatar da cewa, ƙungiyoyin addini da al'umma takwas (8) ne suka shigar da ƙorafe-ƙorafe bayan amsa kiran mai girma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na cewa, duk mai ƙorafi ya kawo a rubuce.
Majalisar ta gayyaci Sheikh Abubakar Shu'aibu Lawal limamin masallacin Triumph, a kan ƙorafe-ƙorafen da aka shigar a kansa ana zarginsa da ya yi ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W.) a karatunsa da ya gabata.
Haka nan, su ma waɗanda suka shigar da ƙorafe-ƙorafen majalisar ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, sai da ta gayyace su, domin jin ta bakin kowanne daga cikinsu.
Honourable Sagagi ya ƙara da cewa, ''Majalisar ta duba ƙorafe-ƙorafen kuma za ta gayyaci kowane ɓangare har da Triumph domin jin ta bakinsa.'' Ya kuma ce, ''Majalisar za ta yi aiki tsakaninta da Allah, da kuma ba wa gwamnati shawarar da ta dace.''

Post a Comment

Previous Post Next Post