Zamfara: ’Yan Bindiga Sun Kashe Liman Da Wasu Masallata 5; Sama Da Masu Hakar Ma’adinai 100 Sun Rasa Rayuka A Ruftawar Rami


Harin Masallaci A Tsafe

Wani hari na ’yan bindiga ya sake girgiza jihar Zamfara, bayan da aka kashe aƙalla mutum biyar ciki har da limamin masallaci a ƙauyen Ƴandoton Daji ƙaramar hukumar Tsafe.


Shaidu sun ce maharan sun kutsa cikin garin ne da safiyar juma'a lokacin da ake gudanar da sallar asuba, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi.

A cewar wani mazaunin ƙauyen mai suna Inuwa Falke, ’yan bindigar sun yi amfani da ruwan sama wajen shigowa kauyen ba tare da an lura da su ba.
“Ba mu ankara da motsinsu ba, sai kawai muka ji harbe-harbe. Na tsira ne kawai saboda ban samu damar zuwa salla ba saboda ruwan sama. Da na je kuwa, da ni ma na fada cikin wadanda aka kashe,” in ji shi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kashe mutum biyar nan take, yayin da suka jikkata wasu da dama tare da yin garkuwa da adadi da ba a san yawansu ba daga cikin masu ibada, sannan suka yi awon gaba da su zuwa dazuka.

Wani shaidar da bai so a bayyana sunansa ba ya bayyana lamarin da cewa “dabbanci ne kuma rashin imani,” yana mai ƙara da cewa waɗanda suka ji rauni suna samun kulawa a asibiti.

Wannan mummunan hari ya zo ne kasa da mako guda bayan makamancin haka a kauyen Gidan Turbe, inda aka yi garkuwa da sama da mutum 40 a lokacin sallar asuba. Ana kyautata zaton an kaisu maboyar ’yan bindiga a dazukan Gohori.


Ruftawar Ramin Hƙar Zinariya A Maru

A wani lamari mai kama da bala’i, sama da mutane 100 suka rasa rayukansu dalilin ruftawar da wani ramin haƙar zinariya ya yi a ƙauyen Kadauri, ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne ranar Alhamis, inda ramin ya rufe ɗaruruwan masu haƙar  ma’adinai da ke cikin sa. An kuma ruwaito cewa ƙoƙarin ceto ya janyo karin mutuwa, saboda wasu daga cikin masu aikin ceto sun mutu yayin da suke ƙoƙarin tsamo waɗanda suka maƙale.

Kawo yanzu, an tono gawarwaki daga ramin a ƙauyen Mekwanegga, kuma aka mayar da su garuruwansu domin yin jana’iza.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Yazid, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ba a iya tantance adadin mutanen da suka mutu ba tukunna saboda aikin ceto yana ci gaba.
“Ko da safiyar yau, an sake fitar da gawarwaki da dama daga ramin,” in ji shi.

Sai dai kuma, kakakin ’yan sandan ya bayyana cewa rundunar ba ta samu rahoton tabbatar da harin masallacin daga ofishin ’yan sanda na Tsafe ba tukuna.

Post a Comment

Previous Post Next Post