Hugo Ekitike Ya Bar Baya Da Kura a Wasan EFL Cup

Ɗan wasan gaban Liverpool Hugo Ekitike ya zura ƙwallon da ta dawo da ƙungiyar ta Liverpool ci gaba da jagorantar wasan a lokacin da ake 1 - 1 tsakaninsu da Southampton. Hugo ya ci ƙwallon ne a mintunan ƙarshe 85, kuma ya samu jan kati, sakamakon murnar cin ƙwallo da ya yi ta hanyar tuɓe rigarsa da ya yi a cikin fili.

Hugo Ekitike

Abin da ba mu tabbaci shi ne, shin yana sane ya aikata haka ko kuwa mantawa ya yi, ko ma dai wanne ne, wannan dalilin ya jefa ƙungiyar ta Liverpool tsaka mai wuya. Kuma hukuncin wannan jan katin zai bi shi har wasan da ƙungiyar Liverpool ɗin za ta buga na Premier League.

Daga ƙarshe dai, wasan ya tashi 1 : 2, inda ƙungiyar Liverpool ɗin ta doke abokiyar karawar tata da ci biyu da ɗaya, wanda Alexander Isaak ne ya ci ƙwallo ta farko tun a mintuna 43 da fara wasan, wanda kuma ita ce ƙwallonsa ta farko tun bayan da ya baro tsohuwar ƙungiyarsa ta Newcastle ana dab da rufe kasuwar saye da sayarwa ta Ingila, Hugo Ekitike kuma ya ci kwallo ta biyu a mintuna na 85 sannan ya amshi jan kati a mintuna na 86.

Click HERE to read in English.

Abu-Ubaida Sani

I provide language services such as translation, transcription, proofreading, interpretation, etc in the Hausa language. I also outsource in Pidgin, Yoruba, Igbo, Fulah, and Kanuri. Contact me through email: abuubaidasani5@gmail.com or WhatsApp: +2348133529736

Post a Comment

Previous Post Next Post