Kasar Saudiyya Ta Saki Tsohon Limamin Harami Sheikh Dr. Saleh Al-Talib Bayan Kwashe Shekaru Bakwai A Gidan Gyaran Hali

Rohotanni sun bayyana cewa an saki ɗaya daga cikin manyan limaman masallacin Harami na Saudiyya, Sheikh Dr. Saleh Al-Talib da ƙasar ta Saudiyya ta ɗaure a gidan kurkuku tun a shekarar 2018. Ƙasar ta kama Limamin ne da laifi  lokacin da ya gudanar da wata sallar Jumma'a, inda a cikin huɗubarsa yake bayyana aikin Musulunci na kawar da ayyukan baɗala da ake aiwatarwa a bayyane, wanda ƙasar ta fahimci kamar kai tsaye yana suka ne zuwa ga Ma'aikatar Nishaɗantar da al'umma ta ƙasar Saudiyyar ne, wanda hakan ya jaza aka yanke masa hukuncin shekaru 10.

Kamar yadda rahotanni da dama suka rawaito, yanzun babban Shehin malamin zai ci gaba da shan ɗaurin talala a gidansa na cikon shekaru ukun da suka rage masa. Wannan duk cikon umarni ne a kan laifin da ake zarginsa da aikatawa.

Sheikh Dr. Saleh Al-Talib

Post a Comment

Previous Post Next Post