Shahararren ɗan ƙwallon tsakiyar nan na ƙasar Sifaniya, ɗan tsohuwar ƙungiyar Barcelona, wanda yake taka leda yanzu a Amurika a ƙungiyar Inter Miami mai suna Sergio Bisquet, ya yanke shawarar ajiye ƙwallon da zarar wannan kakar wasannin ta zo ƙarshe.
Sergio Bisquet ya taka leda tare da Lionel Messi a Barcelona, wanda daga baya, bayan Messi ya bar Barcelona ya tafi ƙungiyar PSG, ƙarshe kuma ya koma Inter Miami, Bisquet bai ɓata lokaci ba ya ayyana aniyarsa ta sake jonewa da gwarzon ɗan ƙwallon duniyar wanda ya lashe kyautar Ballon D'or sau bakwai, yanzu dai ya bayyana ajiye Tamaula ba zato ba tsammani.
Tags
Wasanni