Sojoji Sun Kama Waɗanda Ake Zargin ’Yan Bindiga Ne 5, Sun Gano Makamai a Kwara


Sojojin rundunar Najeriya sun cafke mutane biyar da ake zargi da aikata garkuwa da mutane a wani shingen bincike da aka kafa a kan titin Share, ƙaramar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara.

An tare su ne a ranar Alhamis yayin da suke tafiya cikin wata mota ƙirar Golf, inda aka gano bindigogi kirar AK-47 guda shida da aka ɓoye ƙarƙashin buhuhuwan gawayi. Jami'an tsaro sun tabbatar da cewa ana ci gaba da yi musu tambayoyi.

Wannan kamen ya biyo bayan kama wasu mutum shida da ake zargi a ranar Laraba a kusa da Babanla, inda ake kyautata zaton suna aiki a matsayin masu ɗaukar kayan abinci da mai domin samar wa ’yan ta’adda masu garkuwa da mutane.

Rahotanni sun nuna cewa, an cafke su ne yayin wani aikin sintiri da masu sa-kai na gwamnati suka gudanar a yankin. An miƙa waɗanda ake zargin zuwa hedikwatar ’yan sanda ta jihar Kwara da ke Ilorin domin ci gaba da bincike.

A wani al’amari da ya faru a ranar Talata, an kai farmaki na haɗin guiwa da masu sa kai a yankin Omu Aran–Eruku, wanda ya yi sanadin hallaka wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne. An gano babura guda shida, bindigogi masu sarrafa kansu, da ƙundun bindigogi ɗauke da harsasai daga maboyarsu.

Haka kuma jami’an tsaro sun ceto mata huɗu da samari biyu da ake zargin sun shiga hannun ’yan bindiga. An mika su ga sashen ’yan sanda na Omu Aran.

Post a Comment

Previous Post Next Post