Ibrahim Traoré, matashin shugaban sojin Burkina Faso, na ci gaba da fitowa a matsayin jagora mai kawo sauyi wanda masu sharhi ke ganin ya wuce batun siyasar ƙasa kawai. Bayan ya kori dakarun Faransa daga ƙasar tare da mayar da alaƙa ga Rasha, Traoré ya bayyana shirinsa a matsayin juyin-juya-hali da ya ta’allaƙa da ‘yancin tattalin arziki, haɗin kan yankin da kuma ɗabi’ar zamantakewa ta addini.
Rahotanni sun nuna cewa Traoré ya yi tasiri daga ra’ayin marigayi Samir Amin, masanin tattalin arzikin Masar-Faransa, wanda ya jaddada cewa Afirka dole ta ɓalle daga tsarin tattalin arzikin duniya idan har tana son samun cikakken ‘yanci. Bisa wannan manufa, gwamnatinsa ta sake fasalin yarjejeniyar haƙar zinariya da manyan kamfanoni na ƙasashen ƙetare, sannan ta mayar da hankali kan noma da samar da abinci na cikin gida. Haka kuma, ya tallafa wajen kafa “Ƙawancen ƙasashen Sahel” tare da Mali da Nijar domin ƙarfafa dogaro da kai a yankin.
A ɓangaren tsaro, korar sojojin Faransa da kuma tallafin da yake baiwa “Sojojin sa-kai na Kare Ƙasa” na nuna manufarsa ta ɗaukar ragamar tsaro daga Wagadugu maimakon daga Paris.
Wani salo na musamman a tsarin mulkinsa shi ne yadda yake jingina da addinin Musulunci a matsayin tushe na sahihancin shugabanci. Traoré na gabatar da Musulunci a matsayin hanyar ladabi, haɗin kai da kare ƙasa.
Da wannan haɗin guiwa na gyaran tattalin arziki, ƙarfafa haɗin kan yankin, da kafa ginshiƙan ɗabi’a, Traoré ya fito da wani sabon hangen nesa na mulkin Afirka wanda ke neman ‘yanci a siyasa, tattalin arziki, al’adu da kuma ruhi.