Majalisar Dinkin Duniya Ta Gargadi Cewa AI Na Iya Fadada Talauci Tsakanin Kasashe

 Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta fito da sabon rahoto inda ta gargaɗi cewa ci gaban fasahar ƙirƙirarriyar basira (AI) zai iya ƙara zurfafa giɓin da ke tsakanin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi da waɗanda ke fama da talauci. A cewar UN, fasahar na tashi da sauri fiye da yadda yawancin gwamnatoci suka shirya, abin da zai iya barin ƙasashe marasa ƙarfin tattalin arziki a baya.

Ƙirƙirarriyar basira

Rahoton ya nuna cewa ƙasashe masu ƙarfi na zuba jari sosai a fannin AI, daga bincike, gina manyan cibiyoyin kwamfuta zuwa horas da ƙwararru, wanda ke ba su babbar dama wajen amfani da fasahar don bunƙasa tattalin arziƙin su. Sai dai ƙasashe masu tasowa ba su da isassun kayan aiki ko kuɗin da za su bi sahun waɗanda suka riga su gaba.

UN ta kuma ce akwai barazana mai girma cewa fasahar AI za ta iya tattara iko a hannun manyan ƙasashe da kamfanoni kaɗan da suke da sararin tattara bayanai da manyan injunan kwamfuta. Wannan kuwa na iya bai wa ƙarfin tattalin arzikin ƙasashe masu ci gaba damar rinjayar kasuwanni da tsaron duniya ta yadda ƙasashe marasa ƙarfi ba za su iya tsayawa kafada-da-kafada da su ba.

Saboda haka ne UN ta shawarci gwamnatoci su gaggauta kafa manufofi da tsarin da zai bai wa kowa damar amfani da fasahar cikin adalci. Ta ce ya zama wajibi a zuba jari wajen horas da matasa, gina cibiyoyin intanet masu ƙarfi, da samar da dokoki da za su kare al’umma ba tare da hana cigaba ba.

Duk da haka, Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada cewa AI na da damar kawo ci gaba mai yawa idan aka sarrafa ta da hikima. Ta ce haɗin kai tsakanin ƙasashe, gaskiya da buɗaɗɗen aiki tare sune makamin da zai hana AI zama wata sabuwar hanyar faɗaɗa rashin daidaito a duniya.

Post a Comment

Previous Post Next Post