Tinubu Ya Naɗa C.G. Musa Ministan Tsaron Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tura sunan tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa, mai ritaya zuwa majalisar dattawan ƙasar domin tantance shi a matsayin ministan tsaro.

A wata takarda da Tinubu ya aika, ya buƙaci majalisar ta tantance Musa a matsayin wanda zai maye gurbin Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus a ranar Litinin, kamar yadda mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.

A ranar Litinin 1 ga watan Disamba ne Ministan Tsaron Najeriya Mohammad Badaru Abubakar ya sauka daga muƙaminsa, sannan Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da matakin.

A wata sanarwa da mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanguga ya fitar ranar Litinin ɗin da daddare, ya ce Badaru ya sanar da ajiye aikin nasa ne a takardar da ya aika wa shugaba Bola Tinubu, inda sanarwar ta ƙara da cewa Badaru ya ajiye aikin ne bisa dalilai na neman lafiya.

Sanarwar ta kuma ce shugaban na Najeriya ya amince da ajiye aikin ministan tare da gode masa kan gudumawar da ya bayar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalolin tsaro, musamman dawowar garkuwa da mutane a yankin arewacin ƙasar, musamman a makarantu da kuma hare-hare a wasu jihohi, ciki har da jihar Kano da ba a saba ganin haka ba a baya.

A watan jiya ne ƴanbindiga suka sace ɗalibai 25 a jihar Kebbi, sannan aka sace wasu kimanin 300 a jihar Neja, da kuma wasu a wasu jihohin duk da cewa an ceto na Kebbi baki ɗayansu.

Haka an samu rahoton kashe-kashe, ciki har da jihar Borno inda aka kashe wasu manoma, da kuma hafsan sojin ƙasa, Birgediya Janar Uba Musa da ake zaton ƴan ISAWP sun kashe, duk da cewa rundunar sojin ƙasa ba ta tabbatar ba har zuwa yanzu.

A makon jiya ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalolin tsaro a ƙasar, inda ya ɗauki matakai guda da ya ce za a yi domin daƙile matsalolin da ƙasar ke fuskanta.

Najeriya ta ƙara tsaka mai wuya ne bayan da aka fara yaɗa zargin yi wa Kiristocin ƙasar kisan kiyashi, lamarin da Shugaban Amurka Donald Trump ya karɓa hannu biyu-biyu, har ya yi barazanar tura sojoji zuwa Najeriya domin "su yi yaƙi da ta'addanci."

Bayan barazanar ta Trump ne aka kai harin kan masu ibada a wani coci da ke jihar Kwara, sannan aka yi garkuwa da ɗaliban wata makarantar Katolika a jihar Neja da satar mutane a jihar Kogi, lamarin da ya ƙara fama ciwon da ƙasar ke fama da shi na tsaro.

Sai dai Tinubu ya tura tawaga ta musamman a ƙarƙashin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu zuwa Amurka domin ganawa da hukumomin tsaron ƙasar, inda suka tattauna kan zargin na gwamnatin Amurka, da kuma ba ƙasar bayanin "haƙiƙanin abubuwan da ke faruwa a ƙasar."

Sai dai har yanzu ba a samu cikakken bayanin abubuwan da suka cimmawa ba, amma fadar shugaban ƙasar ta bayyana cewa sun cimma wasu matakai, sannan ƙasar ta sanar da kafa kwamitin ƴan ƙasar a ƙarƙashin Ribadu domin ganawa da wakilan da Amurka za ta kafa domin su yi aiki tare da domin magance matsalar da Najeriya ke fuskanta.

Sai dai duk kafin nan, ƙasar ta daɗe tana fama da matsalolin tsaro, inda ƙasar ke fama da ƙungiyoyin ƴanbindiga da suke addabar sassan ƙasar daban-daban, lamarin da ya sa ƴan ƙasar ke ta kira da a ɗauki mataki.

Post a Comment

Previous Post Next Post