Abu Uku Da Gwamnonin Arewa Suka Cimma kan Tsaro

Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya 19 sun fitar da wasu abubuwa guda 3 da suka ce za su mayar da hankali a kai domin tunkarar matsalar tsaron da ta dabaibaye yankin.

Wannan ya biyo bayan taron da ƙungiyar gwamnonin 19 ta yi a Kaduna wanda aka kammala shi ranar Litinin.

Taron ya samu halartar gwamnoni da sarakunan yankin.

Ƴansandan jiha

Ƙungiyar gwamnonin ba tare da ragin ɗaka ba ta amince da kafa ƴansandan jiha, inda gwamnonin suka shawarci ƴan Majalisar Dokokin Najeriya da ta jihohi na yankin na Arewa da su gaggauta aikin da zai tabbatar da samun ƴansandan jiha.

Haƙar ma'adanai

Ƙungiyar gwamnonin ta ce za ta sharwarci shugaban ƙasa domin ya bai wa ministan albarkatun ƙasa umarnin dakatar da dukkannin ayyukan haƙar ma'adanai a yankin arewacin ƙasar har na tsawon watanni shida domin samun damar tantance aikin.

Hakan zai bai wa gwamnonin jihohin da ake haƙar ma'adan damar tuntuɓa da gano masu ayyukan haƙar ma'adanai da ke yi ba bisa ƙa'ida ba.

Gidauniyar Tsaro

Gwamnonin kuma a tsakaninsu sun amince su samar da wata gidauniya da suka kira Gidauniyar Tsaro ta Arewa domin tunkarar matsalar da yankin ke fuskanta.

Ƙungiyar ta ce kowace jiha ta amince za ta rinƙa zuba naira biliyan guda a asusun, inda za a rinƙa cire kuɗin tun kafin ma ya kai ga asusun jiha.

Sai dai gwamnonin ba su yi cikakken bayanin yadda za su riƙa kashe kuɗin.

Dama dai masana tsaro sun jima suna bayar da shawarar aiki tare tsakanin duka jihohin arewa domin magance matsalar tsaron da yankin ke fuskanta.

Post a Comment

Previous Post Next Post