Germany Ta Ki Amincewa Da Cewa Israel Na Aikata Kisan Kare-Dangi a Gaza

 Hukumar gwamnatin Jamus ta sake jaddada matsayarta cewa ba ta ganin ayyukan Isra’ila a zirin Gaza a matsayin “genocide” ko kisan kare-dangi, duk da sukar da ake yi a duniya. A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Jamus ba ta ganin wani alamar cewa Isra’ila na da niyyar rusa al’ummar Palestine gaba ɗaya, kamar yadda ake zargi a kotun duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama.

Gaza

Sai dai duk da wannan matsayi, gwamnatin Jamus ta fara ɗaukar matakai na taka-tsantsan game da dangantakarta da Isra’ila. A kwanakin baya, Berlin ta ɗage sayar da wasu makamai zuwa Isra’ila, tare da kira ga gwamnati ta tabbatar da cewa agajin jin ƙai ya riƙa shiga Gaza ba tare da ƙuntatawa ba. Firayim Minista Friedrich Merz ma ya ce abin da ke faruwa a Gaza “ya wuce misali” kuma lokaci ya yi da a nemi cikakkiyar tsagaita wuta.

A gefe guda kuwa, ra’ayin jama’a a Jamus ya sha bamban da na gwamnati. Binciken da aka gudanar ya nuna cewa sama da rabin ‘yan ƙasar, kimanin kashi 62 cikin ɗari, suna ganin ayyukan da Isra’ila ke yi a Gaza suna da siffofin kisan ƙare-dangi. Wasu ma na goyon bayan EU ta ɗauki matakin takunkumi kan Isra’ila tare da gane ƙasar Palestine a matsayin mai cin gashin kanta domin dakatar da tashin hankali.

Manyan masana kan siyasar Turai na ganin cewa wannan sabanin ra’ayi na kara matsa lamba a kan gwamnatin Jamus, wacce ta daɗe tana goyon bayan Isra’ila saboda tarihin ƙasar da abin da ya faru a lokacin Holocaust. Wasu sun ce idan Berlin ta canza matsayi, hakan zai iya sauya yadda ƙasashen Turai ke mu’amala da rikicin Gaza baki ɗaya.

Yanzu haka ana ganin Jamus na cikin matsanancin hali tsakanin kiyaye dangantakarta da Isra’ila da kuma ɗaukar matakin da zai daidaita ra’ayin cikin gida da na ƙasashen duniya. Masu sharhi na cewa matakin Jamus a watanni masu zuwa zai taka muhimmiyar rawa wajen tantance ko Turai za ta matsa lamba ga Isra’ila ko kuwa za ta ci gaba da tsayawa a gefe guda.

Post a Comment

Previous Post Next Post