Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kaddamar da manyan sauye-sauyen da ke canza tsarin ilimi a Najeriya, musamman a fannonin da suka shafi ingantawa da sake fasalin manhaja. Ya yi wannan bayani ne a hira da Imoleayo Oyedeyi, inda ya duba shekararsa ta farko a matsayin Ministan Ilimi na 31.
"Mun Farfado da Ilimin Fasaha da Sana’o’i"
A cewar ministan, babban aikin da suka fara shi ne dawo da karfin ilimin fasaha da koyon sana’o’i (TVET) a makarantun Najeriya. Ya ce gwamnati ta samu gagarumin nasara wajen sake jawo hankalin matasa zuwa wannan fanni, wanda ya kira “tushen ci gaban kowace al’umma”.
Alausa ya bayyana cewa sama da dalibai 250,000 ne suka shiga rukuni na farko na shirin koyar da sana’o’i ta hanyar atisaye, tare da shirin kai wa dalibai miliyan 1 cikin shekaru uku masu zuwa. Gwamnati na biyan kowanne ɗalibi N22,500 a wata a matsayin tallafi, yayin da cibiyoyin horarwa ke karɓar N45,000 domin kula da su.
Ya ce gwamnatin ta haɗa hannu da masu zaman kansu domin ƙara samar da kudaden inganta bita, sayen kayan aiki na zamani, da ɗaukar ƙwararrun malamai.
Magance Matsalolin Da Aka Taras
Ministan ya bayyana cewa lokacin da suka karɓi ragamar ma’aikatar, akwai matsaloli masu yawa da suka haɗa da:
-
lalacewar gine-ginen makarantu
-
yawan yajin aikin jami’o’i
-
cin hanci da maguɗin jarabawa
-
ƙarancin malamai masu inganci
-
raguwar sha’awar matasa ga ilimin sana’o’i
Ya ce yanzu kusan dukkan waɗannan matsalolin an shawo kansu. A cewarsa:
-
WAEC da NECO za su mayar da Computer-Based Test (CBT) gaba ɗaya daga 2026, don murkushe maguɗi
-
an gyara kusan makarantu 20,000 na firamare da sakandare tare da samar da su da wutar solar da fasahar zamani
-
an samar da tsarin koyar da malamai ta hanyar dijital
-
an kawar da yajin aiki a jami’o’i a zangon karatu na baya-bayan nan
Alausa ya ce gwamnatin Tinubu ta cimma “matsakaicin mafi girman karin albashi” da aka taba bai wa malaman jami’a a tarihin ƙasar.
Faɗaɗa Guraben Jami’o’i da Sauya Dokokin Shiga
A cewar ministan, gwamnatin ta ƙara yawan ɗaliban da jami’o’i za su iya karɓa daga 700,000 zuwa 1.2 miliyan, tare da sake fasalin dokar cancantar shiga.
Ya ce ba lallai sai ɗalibi ya samu credit a Turanci ba idan ba shi da alaƙa da fannin da zai karanta. Misali, ɗalibin injiniya ko kimiyya zai fi buƙatar Mathematics da sauran darusan da suka dace da fannin.
Haka kuma, an ninka yawan ɗaliban likitanci, magunguna da jinya, tare da zuba sama da N120bn wajen gina dakunan gwaje-gwaje da sabbin dakunan kwana a makarantu na kiwon lafiya a sassan ƙasar.
"Mun Tarawa Ƙasa Malamai da Ma’aikatan Lafiya da Yawa" Minista
Dangane da matsalar barin ƙasa (japa), Alausa ya ce gwamnati ta fi karkata wajen faɗaɗa guraben karatu da horas da ƙarin ma’aikata. Ya ce:
-
adadin ɗaliban jinya ya tashi daga 28,000 zuwa 130,000 a shekara
-
an ninka yawan ɗaliban likitanci da pharmacy
-
an dakatar da tura malamai zuwa waje don horo, domin mafi yawan su ba sa dawowa
Saboda haka, gwamnati ta zuba jari wajen kafa cibiyoyin ƙwarewa a Najeriya domin duk wasu horo da ake yi a ketare su koma cikin gida.
Soke Dokar Koyarwa da Harshen Gida
Game da asusun gwamnati na soke dokar koyar da darussa da harshen gida daga Primary 1 zuwa 4, Alausa ya ce:
Duk da amfanin koyarwa da harshen uwa, mafi yawan jihohi ba su aiwatar da dokar ba.
Yankuna hudu Kudu maso Yamma, Kudu maso Kudu, Kudu maso Gabas da Arewa ta Tsakiya har yanzu suna amfani da Turanci a matsayin harshen koyarwa gaba ɗaya.
Ya ce wannan rashin daidaiton aiwatarwa ne ya sa gwamnati ta sake duba tsarin.