Rundunar Sojojin Najeriya ta dakatar da dukkan nau’ikan ritayar na doka ko na son rai na jami’anta daga yau, a matsayin wani gaggawon mataki na magance ƙalubalen tsaro da ke ƙara ta’azzara a faɗin ƙasar.
Wani majiya mai ƙarfi daga Hedikwatar Sojoji da ke Abuja ya tabbatar wa Tribune Online cewa an aiko da sabuwar umarnin ne ta wata takarda da Sakataren Soji ya sanya wa hannu a madadin Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu.A cewar takardar, an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da cewa rundunar ta riƙe kwararrun ma’aikata, ta ƙara ƙarfin aiki, da kuma taimakawa wajen faɗaɗa yawan dakarun da ake aiwatarwa a sakamakon dokar ta-baci kan tsaro da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana, wadda ake aiwatarwa ba tare da tangarda ba.
Dokar “Harmonised Terms and Conditions of Service (Officers) 2024” ta tanadi cewa jami’ai kan yi ritaya ne bisa shekaru, ko kammala shekaru 35 na aiki, tare da wasu ƙa’idoji na ƙungiya. Sai dai sashe na 3.10(e) na kundin ya bai wa runduna damar tsawaita lokacin aiki idan hakan na da muhimmanci ga tsaron ƙasa.
Takardar ta kara da cewa bayan ayyana dokar ta-bacin tsaro a ranar 26 ga Nuwamba da kuma umarnin faɗaɗa rundunonin tsaro, ya zama dole a dakatar da ritaya na ɗan lokaci a rundunar soji.
Wadanda matakin ya shafa sun haɗa da jami’an da suka fadi jarabawar karin girma sau uku, waɗanda aka wuce su a teburin karin girma har sau uku, wadanda suka kai iyakar shekaru a mukamansu, wadanda suka fadi jarrabawar sauya fanni sau uku, ko kuma wadanda suka cika shekaru 35 a bakin aiki.
An bai wa jami’an da abin ya shafa damar yin rajistar ci gaba da aiki bayan lokacin da ya kamata su yi ritaya. Amma wadanda ba sa son tsawaitawar, za su iya ci gaba da shirin ritayarsu ta yau da kullum.
Sai dai takardar ta yi gargadin cewa duk jami’in da aka ba wa ƙarin lokaci ba zai sake samun damar ci gaba da hawa mukami ba—ba karin girma, ba horo, ba tallafi, ba aikin waje, kuma ba canjin sashen aiki.
An umurci kwamandoji su tabbatar da isar da umarnin ga jami’ansu tare da kula da yiwuwar faduwar ƙwarin gwiwa da matakin ka iya haifarwa. Rundunar ta ce za a sake duba wannan umarni idan yanayin tsaro ya inganta.
A ƙarshe, takardar ta fayyace cewa kundin “Harmonised Terms and Conditions of Service (Officers) 2024” shi ne tushen doka da rundunar ta dogara da shi wajen dakatar da ritayar na ɗan lokaci.